Tim Cahill ya koma Hangzhou

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kwantaragin Cahill da Shanghai Shenhua ta kare a makon da ya gabata

Tsohon dan wasan tsakiya na Everton, Tim Cahill ya rattaba hannu a kan kwantaragi mai gajeren zango da kungiyar wasa ta Hangzhou Greentown da ke China.

A makon da ya gabata ne dai kwantaragin dan wasan ta kawo karshe da kungiyar Shanghai Shenhua.

Cahill mai shekara 36 ya rubuta a shafinsa na Instagram cewa " na rattaba hannu kan kwantaragi na wata biyar. Saboda haka, gaba za ta yi kyau."

Tim Cahill wanda dan asalin Australia ne ya koma China daga kungiyar wasa ta Red Bulls da ke New York, a 2015.