Za mu hana Luis Suarez sakat - Wenger

Image caption Luis Suarez ya zura kwallaye 25 a gasar La Liga

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger ya ce dole kungiyar ta hana dan wasan Barcelona, Luiz Suarez sakat, idan dai suna son samun nasara a kan Barcelonar.

A ranar Talata ne dai Arsenal za ta karbi bakuncin Barca, a wasa na 16 na zangon farko na gasar zakarun turai ta Champions League.

Arsene Wenger ya ce " Suarez ne yake zaburar da abokan wasansa, a lokacin wasa."

Shi dai Arsene ya yi niyyar sayen Suarez a lokacin yana Liverpool a watan Yulin 2013.

Suarez, mai shekara 29, ya zura kwallaye 25 a gasar La Liga.