Europa League: An ci Celtic tara

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An ci Celtic tarar £13,000m

Sashen kula da da'ar 'yan wasa na hukumar kwallon kafa ta turai, wato Uefa, ya ci tarar kungiyar wasa ta Celtic £13,000 bisa rashin da'ar da magoya bayan kungiyar suka nuna, a lokacin wasansu da Fenerbahce.

Magoya bayan wasan dai sun kunna tartsatsin wuta lokacin da kungiyar ta yi canjaras wato 1-1 da Fenerbahce ranar 10 ga Disamba.

Ko a kakar wasan da ta gabata ma, an ladabtar da kungiyar saboda rashin da'ar da magoya bayanta suka nuna a wasansu da Inter Milan.

An dai tsare magoya bayan kungiyar guda biyar a wannan watan saboda waken wariyar launin fata da suka yi, a lokacin wasan cin kofin kasar Soctland da Celtic din ta yi da Straraer.