FIFA: Mun shirya wa zabe - Infantino

Image caption Dan takarar shugabancin hukumar Fifa, Gianno Infantino

Daya daga cikin 'yan takarar shugabancin hukumar Fifa, Gianno Infantino ya ce idan dai ba gudanar da zaben hukumar Fifa yanzu ba to hukumar ba za ta yi kyau ba.

Abokin karawarsa, Yarima Ali ibn al-Hussain ya nemi da a dakatar da zaben bisa zargin rashin gaskiya.

Amma Gianno Infantino ya ce dole ne a gudanar da zaben kamar yadda aka tsara.

Da yake magana da BBC, Infantino ya ce " idan dai ba mu yi wani abu ba domin dawo wa da Fifa kimarta da ta zube da kuma bunkasa harkar wasan kwallon kafa a duniya, to fa hukumar ba ta da gaba mai kyau."

A makon da ya gabata ne dai hukumar kwallon kafar Ingila ta bayyana goyon bayanta ga Gianno Infantino wanda tsohon babban sakataren hukumar gudanarwa ne na hukumar kwallon kafa ta turai wato Uefa.