Man City: Mangala zai buga wasa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wilfred Bony da Yaya Toure da Eliaquim Mangala

Kociyan Manchester City, Manuel Pellegrini ya yi maraba da dawowar dan wasan kungiyar, Eliaquim Mangala wanda da yake hutun dole sakamakon rauni da ya ji.

A ranar Laraba ne dai kungiyar Dynamo Kiev za ta karbi bakuncin Manchester City a zagaye na 16 na zangon wasa na farko na gasar zakarun turai wato Uefa Champions League.

Da ma dai Pellegrini ya ajiye taurarin 'yan wasansa a inda ya dauko matasa guda shida wadanda suka taka wasan da kungiyar ta kwashi kashinta a hannun Chelsea da ci 5-1, ranar Lahadi.

Yanzu haka, Pellegrini zai zabo 'yan wasan da suka taka masa leda lokacin da kungiyar ta kara da Tottenham City a wasansu na karshe na gasar Premier League.

Tun dai ranar 6 ga Janairu, Eliquim Mangala bai kara wasa ba saboda raunin da ya ji a kafarsa.