Messi ya yi wa Arsene Wenger bazata

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Lionel Messi ya ci kwallaye biyu

Kungiyar wasa ta Barcelona ta lallasa Arsenal da ci 2 da nema a gida, a wasan zango na farko na kasashe 16 na gasar zakarun turai.

Dan wasan Barcelona, Lionel Messi ya jefa kwallaye biyun.

Messin dai ya zura kwallaon farko bayan da Neymar da Suarez suka yi wasan taba-in-taba suka kuma ba wa Messin. Ya kuma jefa ta biyun ne a bugun fanareti sakamakon keta da Flamino ya yi masa a dab da raga.

A ranar Litinin dai kociyan Arsenal, Arsene Wenger ya nuna fargabarsa da dan wasan Barcelona, Suarez wanda ya ce shi ne yake zaburar da sauran abokan wasansa.

Ya kuma sha alwashin hana shi sakat a wasan nasu na ranar Talata.