FA Cup: An kama masu jifa da sulalla

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An fara kama masu jifa da sulalla a filin wasa

'Yan sanda sun kama wasu 'yan kallo wadanda suka jefi dan wasan West Brom, Chris Brunt da sulalla, a lokacin wasan kungiyar da Reading, ranar Asabar.

'Yan kallon dai wadanda ake zargin magoya bayan West Brom din ne, sun jefi Chris Brunt da sulalla, a lokacin da ya shiga cikinsu domin ba wa wani yaro rigarsa.

West Brom dai ta kwashi kashinta a hannun Reading da ci 3-1.

'Yan sandan dai sun ce sun yi kamen ne bisa hadin gwiwa da 'yan sanda Hampshire.

Ita ma Chelsea ta ce za ta sanya takunkumi mai tsanani a kan duk wanda aka samu da laifin jifan 'yan wasan Manchester City, da sulalla a wasan da suka taka a Stamform Bridge, ranar Lahadi.