Arsenal v Barcelona: Suarez ya manta fasfo

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Suarez da Messi da Neymar sun zura kwallaye 91 a tsakaninsu a wannan kakar wasan

Dan wasan gaba na Barcelona, Luiz Suarez ya manta fasfo dinsa a gida, dab da tashin 'yan wasan na Barca zuwa London domin karawa da Arsenal.

Da yammacin ranar Talata ne dai Arsenal da Barcelona za su fafata a wasan zango na daya zagaye na 16 na gasar zakarun turai.

Sai dai kuma dandanan aka aika wani zuwa gidan Suarez din domin dauko masa fasfo din, domin su tashi tare da sauran abokan wasansa.

A ranar Litinin dai kociyan Arsenal, Arsene Wenger ya bayyana firgicinsa dangane da dan wasan wanda ya ce " Suarez ne yake harzuka sauran abokan wasansa saboda haka dole ne su hana shi sakat."

Shi dai Suarez ya zura kwallaye 41 a kakar wasanni ta bana.