FIFA: Blatter da Platini ba su yi nasara ba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Blatter da Platini

Tsohon shugaban hukumar Fifa, Sepp Blatter da shugaban hukumar kwallon kafa ta turai, wanda aka dakatar, Michel Platini ba su samu nasara ba kan kokensu na a dage dakatarwar da aka sanya musu na shekara takwas daga harkokin wasanni.

Sai dai kuma mutanen biyu sun samu an rage tsawon zangon dakatarwar daga shekara takwas zuwa shida.

An dai samu mutanen biyu da laifin rashawa ta kudi £1.3m da Blatter ya ba wa Platini.

Dukkaninsu sun kai kokensu zuwa ga kwamitin koke na hukumar ta fifa domin yin duba ga hukuncin dakatar da su daga harkokin wasanni na shekara 8.

Blatter da ya ce zai daukaka kara zuwa ga kotun kwallon kafa ta duniya, a inda yake cewa " na yi mamakin hukuncin na kwamitin koken na Fifa."