FIFA: Infantino na samun goyon baya

Image caption Gianni Infantino yana samun goyon baya

Hukumar kwallon kafa ta Scotland ta ce za ta kada wa tsohon babban sakataren hukumar kwallon kafa ta turai, Gianni Infantino, a zaben shugaban hukumar Fifa da za a gudanar, a Zurich, ranar Juma'a.

Shugaban hukumar kwallon ta Scotland, Stewart Regan ya ce "infantino ne dan takarar da ya ya fi dacewa wajen dawo wa da hukumar ta fifa kimarta."

A farkon watan nan Fabrairu ma, hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ce Infantinon za ta marawa baya, a zaben.

Infantino, mai shekara 45 zai kalubalanci sauran 'yan takarar hudu da suka hada da Prince Ali bin al-Hussain da Sheikh Salman Bin Ebrahim da Tokyo Sexwale da kuma Jerome Champagne.

A ranar Talata ne dai Yarima Ali bn al-Hussain ya kai kara kotu yana neman da a dakatar da gudanar da zaben ranar Juma'a bisa zargin cewa ba za a yi adalci ba.