Ina nan daram a Liverpool - Sturridge

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Daniel Sturridge tare da kociyansa, Jurgen Klopp

Dan wasan Liverpool, Daniel Sturridge ya ce ba bu inda zai je kuma zai ci gaba da zama a kulob din.

Sturridge dai ya fadi haka ne a lokacin da yake mayar wa masu sukar sa martani masu cewa ba ya son taka leda ne kawai, shi yasa yake lambon yawan samun rauni.

Rahotanni ma na cewa Dan wasan yana son barin Liverpool saboda sukar yawan laulayin da yake yi, sai dai kuma Sturridge ya ce " ina da burin da nake son cimma, a shirye kuma nake da na taimaka wa Liverpool."

Sturridge mai shekara 26 ya kara da cewa " fadin cewa dan wasa ba ya son buga wa kulob dinsa wasa, shi ne abu mafi wulakanci ga dan wasa."

Shi dai Daniel Sturridge wanda ya zo Liverpool daga Chelsea a Janairun 2013, ya buga wasanni 9 ne kawai a kakar wasanni ta bana sakamakon yawan raunin da yake samu.