Buhari ya cika alkawari ga 'yan kwallo

Image caption Shekara 30 ke nan da kungiyar kwallon kafar ta 'yan kasa da 16 ta lashe kofin duniya ta gasar.

Shugaba Buhari na Najeriya ya yi wa 'yan kungiyar kwallo kafa kyauta bayan shekaru 30.

'Yan kungiyar kwallon kafar su ne suka ci gasar 'yan kasa da shekara 16 ta duniya a 1985 a lokacin Buhari na shugaban kasa a mulkin soji.

A lokacin, shugaban ya yi wa 'yan wasan alkawarin gidaje da kuma tallafin karatu idan har suka samu nasara a gasar, amma hakan bai yi wu ba saboda juyin mulki da aka yi masa.

A yanzu da ya sake zama shugaban kasa, ya ba kowannensu kyautar dala goma-goma.

A hirar da BBC ta yi da Salisu Nakande ya ce hakika kyautar shugaban kasa ta kai ga wasunsu, haka shi ma Nduka Ugbade, kyaftin din kungiyar a hirarsa shirin wasanni na BBC ya ce kudinsa ya shiga hannunsa.

Daya daga cikin 'yan kwallon ya ce wannan karamci, zai canza tunanin 'yan kasar game da muhimmancin cika alkawari