Kwalliya ta biya kudin sabulu —Pellegrini

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kociyan Man Man City Manuel Pellegrini ya ce "ina mutunta kowacce gasa amma mun fice daga gasar FA, ba a son ran mu ba"

Kocin Manchester City Manuel Pellegrini ya ce shawararsa ta fifita gasar Champions League a kan gasar FA ta yi rana domin nasarar da suka samu a kan Dynamo ta Kiev.

Pellegrini ya sha suka bisa kashin da kulob din ya sha a wata karawa ranar Lahadi lokacin da Chelsea ta lallasa su da ci 5 da 1.

Sai dai kulob din ya samu nasara a karawar ranar Laraba a karon farko da ci 3 da 1

Pellegrini ya yi canji har sau goma kafin ya fita da karfinsa zuwa Kiev, inda Yaya Toure da David Silva da kuma Sergio Aguero suka fitar da kulob din kunya da cin kwallaye.