Ya kamata a yabawa Sam Allardyce —Bilic

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Sam Allardyce na shirn dawowa West Ham a karshen makon nan.

Kociyan West Ham Slaven Bilic, ya ce ya kamata magoya bayan kulob din su yabawa tsohon kociya Sam Allardyce.

Bilic ya yi wannan kira ne ga magoya bayan kulob din a lokacin a da ake sa ran dawowar tsohon Kociyan zuwa kulob din a karshen makon nan.

Rahotanni na cewa akwai yiwuwar Allardyce ba zai samu kyakkyawar tarba ba, duk da cewa shi ya daga likkafar kulob din kafin ya bar shi a watan Mayun 2015.

Allardyce ba shi da farin jini a tsakanin magoya bayan kulob din saboda salon wasansa.