Gianni Infantino ya zama shugaban Fifa

Image caption Infantino ya zama shugaban Fifa

An zabi dan kasar Switzerland Gianni Infantino a matsayin sabon shugaban hukumar kwallon kafar duniya, Fifa.

Infantino zai maye gurbin Sepp Blatter.

Ya samu kuri'a 115 a zagaye na biyu, inda mutumin da ke biye masa Sheikh Salman bin Ebrahim al-Khalifa ya samu kuri'a 27.

Yarima Ali bin al-Hussein ne ya zo na uku da kuri'a hudu, yayin da Jerome Champagne bai samu ko da kuri'a daya ba.

Tokyo Sexwale ya janye daga takarar kafin a fara kada kuri'a.