Chamberlain zai shafe makonni bai buga wasa ba

Image caption Chamberlain zai yi jinyar makonni

Kociyan kulob din Arsenal Arsene Wenger, ya ce dan wasan tsakiya Alex Oxlade-Chamberlain, ba zai buga wasa ba na tsawon wasu 'yan makonni, sakamakon raunin da ya ji a gwiwa.

Dan wasan mai shekara 22, ya ji raunin ne sakamakon kayar da shi da dan wasan Barcelona Javier Mascherano ya yi a fafatawar da suka yi ranar Talata a wasan gasar zakarun Turai.

Ya fita daga filin wasan Emirates da sandar guragu bayan ci biyu babu ko dayan da aka yi musu na farko.

Mista Wenger ya ce, "Chamberlain ya ji rauni sosai ranar Talata don haka dole ne mu ajiye shi na tsawon wasu makonni."

Ya kara da cewa watakila dan wasan ya shafe makonni biyu ko uku kafin ya dawo.