Manchester City ta dauki League cup

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan wasan Man City na murnar daukar kofi a 2014

Manchester City ta dauki kofin Capital one cup karo na biyu a kakar wasanni uku, bayan da ta doke Liverpool a bugun fanareti.

Mai tsaron ragar Man City, Willy Caballero ne ya ceci kungiyar wasan nasa.

Ya dai hana shigar kwallaye uku daga 'yan wasan Liverpool wato Lucas Keiva da Philppe Coutinho da Adam Lallana.

Yaya Toure ne dai ya jefa kwallon da ba wa Man City nasara a kan Liverpool.