Wa Rooney zai bugawa wasa?

Hakkin mallakar hoto empics
Image caption Wayne Rooney tare da kociyansa na Manchester United, Luis van Gaal

Kociyan Manchester United, Wayne Rooney yana samun sauki amma fa zai buga wa Man United wasa ne ba Ingila ba.

Rooney, mai shekara 30 wanda kyaftin ne na Ingila, ya samu rauni a gwiwarsa, a wasan da Man United din ta buga da Sunderland, ranar 13 ga Fabrairu.

Hakan ne yasa ake da kokanton cewa zai buga wa Ingila wasan sada zumunci da za ta yi da Jamus, a Berlin, ranar 26 ga Maris sannan kuma kwanaki uku bayan nan Ingilar za ta kara Holland, a Wembley.

Van Gaal ya ce "mu zai fara buga wa wasa ba Ingila ba."

Ya zuwa yanzu dai Rooney bai buga wasanni uku ba kuma ba zai buga wasan da Man United din za ta yi da Asenal ba, a ranar Lahadi, a Old Trafford.