Capital One Cup: Daukar kofi ya wanke Pellegrini

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manuel Pellegrini ya daga kofin da suka dauka.

Watakila nan da wata uku kociyan Manchester City, Manuel Pellegrini zai iya barin kulob din kuma ana sa ran Pep Guardiola ne zai maye gurbinsa.

Nasarar da Manchester City ta samu na daukar kofin Capital One Cup na nuna cewa Pellegrini ba zai bar baya da kura ba.

Bayan haka kuma daukar kofin ya wanke Pellegrinin dangane da tsarin da ya bi wajen zabo 'yan wasa wanda ya sha suka a kai.

Yanzu haka, Man City ta dauki kofin Capital One kuma tana matsayi na hudu a teburin gasar Premier duka a lokacin jagorancin Manuel Pelligrini.

A ranar Lahadi ne dai Man City ta dauki kofin Capital One Cup, bayan da ta doke Liverpool a bugun fanareti.