Boyata: Celtic za ta kalubalanci jan kati

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan Celtic, Dedryck Boyata

Kungiyar wasa ta Celtic za ta kalubalanci jan katin da mi busa ya dagawa Dedryck Boyata a wasan da suka tashi canjaras da Hamilton Academical.

Sai dai kuma kociyan kulob din, Ronny Deila ya ba wa dan wasan nasa rashin gaskiya kan abun da ya yi har ya samu jan katin, a inda ya ce ya amince da hukuncin mai busar, Craig Thomson.

To amma kuma Deila ya canja ra'ayinsa bayan da ya kalli hakikanin abin da ya faru a faifan bidiyo.

Ya ce "na kalli abin da ya faru sau da yawa, idan ka ga abin da ya faru ta kowane bari, ba ayi adalci ba." kuma za mu "kalubalanci hukuncin."