Na saka wa Pellegrini - Caballero

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Willy Caballero a lokacin da yake kama kwallo a wasansu da Liverpool na karshe na gasar League one Cup.

Mai tsaron ragar Manchester City Willy Caballero ya ce ya saka wa kocin kungiyar Manuel Pellegrini bisa amincewar da ya yi masa har ya sa suka dauki kofin Capital One a Wembley.

Sau uku dan wansan -- dan kasar Argentina -- yana rike kwallayen da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool yayin da City ta doke Liverpool din da ci 3-1 a bugun fenareti

Caballero, mai shekara 34, ya sha suka bayan Chelsea ta doke City da 5-1 a gasar cin kofin FA a Stamford Bridge a makon jiya.

Dan wasan ya shaida wa BBC cewa, "Yana da matukar muhimmanci a gare ni da na buga wasan karshe."