Everton: Za mu kara zage dantse - Martinez

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kociyan Everton, Roberto Martinez

Kociyan Everton, Robert Martinez ya ce zai iya daukar ragamar nauyin da zai karu a kansa sakamakon hannun jarin da Farhad Moshiri ya saka a kulob din.

Mai kudin nan dan kasar Iran,Moshiri ya sayi kaso 49.9 da jarin Everton.

Martinez ya ce burinsa shi ne ganin kulob din ya cancanci buga wasannin gasar zakarun turai har ma su dauki kofi.

Everton dai ita ce ta 12 a teburin Premier sannan kuma ta je wasan dab-da-na-kusa-da-na karshe na League Cup kafin Man City ta doke ta.

Kulob din ya kai ga wasan-dab-da-na-kusa-da-na-karshe a gasar cin kofin FA, kuma za ta kara da Chelsea, ranar 12 ga Maris.