Arsenal: Chamberlain ba zai buga wasanni ba

Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Dan wasan Arsenal, Alex Oxlade-Chamberlain

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger ya ce dan wasan tsakiya na kulob din, Alex Oxlade-Chamberlain ba zai buga wasanni ba har na makonni shida zuwa takwas.

Dan wasan mai shekara 22 wanda ya ji rauni a gwiwarsa a lokacin wasan da suka tashi 0-2 da Barcelona, a gasar zakarun turai ranar 23 ga Fabrairu.

Arsene Wenger ya ce Alex wana ya bar filin wasan na Emirate a katakon guragu, ba ya bukatar tiyata.

A ranar Laraba ne dai Arsenal za ta karbi bakuncin Swansea a wasan gasar Premier.

Arsenal dai ita ce ta uku a teburin gasar Premeir kuma akwai tazarar maki uku tsakaninta da mai matsayi na biyu wato Tottenham sannan kuma maki biyar tsakaninta da mai matsayi na daya wato Leicester.