Raheem ba zai ci amanarmu ba - Pellegrini

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan wasan Manchester City, Raheem Sterling

Kociyan Manchester City, Manuel Pellegrini ya ce ya yi imani dari bisa dari da cewa sabon dan wasan kungiyar wanda ya taho daga Liverpool, Raheem Sterling ba zai yaudare su ba.

A kashen bazarar da ta gabata ne dai Raheem ya koma Manchester City daga Liverpool a kan kudi £44m.

Wasan da Man City za ta yi da Liverpool ranar Laraba shi ne wasan farko da Raheem din zai gamu da tsohuwar kungiyar tasa, a gasar Premeir.

Hakan ne ya sa Pellegrini ya ce " Na yi imani da Raheem, dari bisa dari, kuma ba ni da shakku a kansa."

A ranar Lahadi ne Man City ta dauki kofin Capital One Cup, bayan da ta doke Liverpool da ci 3-1, a bugun fanareti.