'Ba za mu jure kalaman batanci ba'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugabannin West Ham, David Sullivan da David Gold.

Shugabannin kungiyar wasa ta West Ham, David Sullivan da David Gold sun gargadi magoya bayansu kan kalaman batanci yayin wasan da kungiyar za ta kara da Tottenham, ranar Laraba.

A baya dai 'yan kallo sun yi amfani da kalaban batanci a kan yahudawa.

Magoya bayan Tottenham kuma suna da alaka ta kut da yahudawan Ingila.

Sullivan da Gold a wata sanarwa sun ce " duk wani magoyin baya da aka samu da kalaman batanci da suka jibanci wariyar launin fata ko na kin jinin yahudawa ko kuma ga masu neman jinsi guda, to za a dakatar da su daga kallon wasannin gaba."

West Ham dai ta kasance ta shida a teburin gasar Premier yayin da ita kuma Tottenham ta ke a matsayi na biyu a teburin.