European Super League: Arsenal ta yi suka

Image caption 'Yan wasan Arsenal

Kungiyar wasa ta Arsenal ta ce ba ta amince da kafa wata sabuwar gasar kwallon kafa ba ta European Super League da ake hasashen kafawa.

An fara hasashen kafa sabuwar gasar ne bayan taron da shugabannin Arsenal da Chelsea da Liverpool da Manchester City da Manchester United, suka yi ranar Talata.

Wakili daga hukumar gasar cin kofin zakarun turai,ICC na daga cikin shugabannin da suka halarci taron.

Mai magana da yawun Arsenal ya ce " an tattauna ne kan hukumar gasar zakarun turai ta ICC da kuma jadawalin shirya gasar wasanni."

Sai dai kuma ana cewa batun kafa sabuwar gasar ta European Super League ba zai rasa nasaba da kyashin da wasu kungiyoyin kasashen turai suke yi wa gasar Premeir ba saboda irin karfin tattalin arzikin da take da shi.