Kotu ta samu Johnson da laifin lalata yarinya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Adam Johnson dai ya amince da simbantar yarinyar da ake tuhumar sa da yin lalata da ita.

Kotu ta samu tsohon dan wasan Sunderland, Adam Johnson da laifin taba yarinya 'yar shekara 15, amma ba jima'i ba.

Tun da fari dai Adam ya amince da cewa ya simbanci yarinyar amma yaki amincewa da wasu tuhume-tuhume guda biyu masu alaka da saduwa.

Sai dai kuma yarinyar ta ce Johnson "ya sanya hannu a cikin kamfanta," kuma ta biya masa bukata amma ta amfani da bakinta.

Mai shari'ar, Jonathan Rose ya ce Jonson ka iya fuskantar zaman gidan yari saboda haka ya kamata ya yi ban kwana da 'yarsa.

A wata sanarwa da wadda ake tuhumar Johnson din da lalatawa, ta ce ta dade tana fuskantar tashin hankali tun bayan haduwarta da Johnson.