Platini ya daukaka kara kan dakatarwa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Michel Platini da Sepp Blatter

Tsohon shugaban hukumar kwallon turai, Michel Platini ya dauka kara zuwa kotun wasanni ta duniya danagen da dakatarwar da aka yi masa daga harkokin wasanni na shekara shida.

An dai dakatar da Platini ne tare da tsohon shugaban hukumar Fifa, Sepp Blatter, daga harkokin wasanni na tsawon shekara takwas kowannensu, bayan da aka same su da laifin bayarwa da karbar na goro na kudi £1.3m.

Amma daga baya an rage musu wa'adin daga shekara takwas zuwa shida.

Sai dai shi Platini yana neman da a soke hukuncin baki dayansa.