Charlie Austin zai yi jinya mai tsawo

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Charlie Austin

Kocin Southamton, Ronald Loeman, ya ce dan wasan gaba na kungiyar, Charlie Austin, zai yi jinya ta makonni da dama sakamakon ciwon da ya ji a cinyarsa.

Austin ya samu raunin ne a wasan da kungiyar ta sha kashi a hannun Bournemouth da ci 2-0 ranar Talata, inda ya rika dingishi tsawon sa'a daya.

Dan wasan mai shekaru 26, ya koma kungiyar ta Southamton ne daga QPR a watan Janairu, kuma shi ne ya ci kwallon da ta ba su nasara a kan kungiyar Manchester United a wasansa na farko.

Sai dai bai zura kwallo a raga ba a wasanni hudu da ya buga daga baya.