Skiing: Vonn ta karye

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Lindsey Vonn a lokacin wasannin Olympics

'Yar wasan zamiya mai rike da kambu ta duniya, Lindsey Vonn ba za ta yi wasanni ba a wannan kakar saboda karayar da ta samu.

A ranar Asabar ne dai 'yar wasan 'yar kasar Amurka, mai shekara 31 ta samu raunin a lokacin gasar zamiya a Andorra.

Duk da haka dai 'yar wasan ta ci gaba da wasan da haka washe gari, kuma ta ma kara sauri har ma ta samu maki 28.

Vonn ta ce " Ba zan iya yin wasannin gasar zakarun zamiya ta duniya da za a yi a Moritz badi, da kuma wasannin tsalle-tsalle a South Korea, shekaru biyu masu zuwa."