Leicester ta samu ribar Fam miliyan 26

Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Karawar Leicester da Arsenal a gasar Premier ta bana.

Kungiyar Leicester City ta sanar da samun ribar Fam miliyan Ashirin da shida da dubu dari hudu kafin haraji, a shekarar 2015, idan aka kwatanta da hasarar Fam miliyan ashirin da dubu dari takwas da ta yi a shekarar 2013 zuwa 2014.

A sanarwar da kungiyar ta fitar a shafinta na intanet, Leicester ta ce shekara 2014 zuwa 2015 su ne shekaru ma fi sa'a a tarihin samun kudin kulob din.

Samun kudin kungiyar ya tashi daga fam miliyan talatin da daya da dubu dari biyu a shekara ta 2013-14 zuwa Fam miliyan dari hudu da dubu dari hudu.

Alkaluman wadanda suka shiga kallon wasan kulob din ya karu daga fiye da dubu 25 zuwa fiye da fiye da dubu 31 a kakar wasan kulob din na farko a matsayin su na kan gaba a gasar Premier a shekaru goma.