Tennis: Andy da Jamie sun doke Japan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Andy Murray, dan wasan Tennis na Birtaniya

Andy da Jamie Murray, a wasan hadin gwiwa sun doke Japan da ci 2-1 a zagayen farko na gasar Davis Cup da ake yi a Birmingham.

Andy da Jamie Murray din dai sai ba wa Yoshihito Nishioka da Yasutaka Uchiyama, kashi da ci 6-3 da 6-2 da 6-4.

Andy Murray zai hadu da Kei Nishikori, mai matsayi na 6 a duniya, ranar Lahadi

Shi kuma Evans mai matsayi na 157 zai fafata da mai matsayi na 87, Taro Daniel.