Liverpool ta tsira da kyar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Christian Benteke ne ya ci kwallo ta biyu a bugun fanareti

Kulob din Liverpool ya samu nasarar cin kungiyar Crystal Palace 2-1 bayan da Christian Benteke ya jefa kwallo ta biyu a dukan fanareti.

Dan wasan Crystal Palace, Damien Delaney ne ya yi wa Benteke keta a dab da raga abin da yasa mai busa ya ba da daman bugun fanareti.

Tun da farko dai dan wasan Crystal Palace, Joe Ledley ne ya fara jefa kwallon farko a ragar Liverpool a minti na 48 na wasa.

A minti na 62 ne kuma dan wasan Liverpool, James Milner ya samu yelon kati, abin da ya yi sanadiyyar fitarsa daga wasan.

Roberto Firminho ne ya farkewa Liverpool kafin bugun fanaretin da Christian Benteke ya yi.