Tennis: Watson ta je wasan karshe

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yar wasan tennis, Heather Watson

'Yar Birtaniya mai matsayi na biyu a wasan Tennis, Heather Watson ta cancanci zuwa wasan karshe na gasar Monterrey Open, bayan da ta doke 'yar Faransa, Caroline Garcia da ci 6-1 da 6-2.

'Yar wasan mai shekara 23, ta kama dukkannin kwallo biyar da Caroline ta buga mata.

Yanzu haka Watson za ta fafata da 'yar Belgium Kirsten Flipkens ranar Lahadi a wasan karshe.

Watson dai ta lashe gasar Japan Open ta 2012 da kuma gasar Hobart International a wata Janairu na 2015.