West Brom ta doke Manchester United

Hakkin mallakar hoto allsport
Image caption van Gaal da sauran shugabannin Man United

A karon farko a tsawon shekara 32, kungiyar wasa ta West Brom ta doke Manchester United da ci 1-0.

Dan wasan West Brom, Salomon Random ne ya jefa kwallo dayar mai ban haushi a ragar Man United jim kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Manchester United dai ta yi wasa da 'yan wasa goma ne, bayan da aka yi waje da Mata sakamakon samun yelon kati guda biyu da ya yi.

Har yanzu dai Manchester United din ba ta samu damar komawa mazauninta na biyar ba da ta dade a kai na teburin gasar Premier.