Fatana na zamo kociyar Arsenal - Zaidi

Image caption Annie Zaidi, kociyar Leicester City ajin mata 'yan kasa da shekara 11

Annie Zaidi, kociyar kungiyar kwallon kafa ce kuma musulma 'yar asalin yankin kudancin Asiya.

Ta samu takardar shedar zama kociya ta FA mataki na biyu, sannan kuma tana kokarin samun shedar Uefa aji na biyu.

Zaidi tana cikin harkokin kwalejin koya kwallon kafa ta Championship sannan kuma ita ce babbar kociyar kungiyar Leicester City, ajin mata 'yan kasa da shekara 11.

Annie wadda take goyon bayan Arsenal ta ce burinta shi ne zamowa kociyar ta Arsenal.

Sai dai kuma ta ce ta fuskanci kalubale iri-iri da suka hada da wariyar launin fata, da ta kasancewarta mace kuma musulma.