Premeir League: Ko Leicester za ta iya daukar kofi?

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kociyan Leicester, Claudio Ranieri da dan wasan kungiyar Riyadh Maharez.

Masu sharhi kan harkokin wasanni sun sha fadin cewa " Leicester ta yi rawar gani amma ba za ta iya kai wa ga daukar kofi ba."

An dade dai ana irin wannan shaci fadin, to amma zai gashi Leicester tana neman ba da mamaki.

Yanzu dai an buga wasanni 29 daga cikin 38, kuma twasannin biyar ne kawai kungiyar ba ta yi nasara ba sannan ta yi canjaras guda biyu, sai kuma doke West Ham da ta yi a gida da ci 2-1, ranar 4 ga Afrilu.

Hakan na nufin Leicester wadda ta kasance a kasan teburin Premier a kakar wasa ta 2014-2015, yanzu ta ci wasanni 24 a cikin 38 da ta buga.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan gaba na Leicester, Jamie Vardy.

kasancewarta a saman teburin Premier da tazarar maki 5 tsakaninta da mai biye mata wato Tottenham sannan kuma ta ba wa Manchester City tazarar maki 11.

Wasanni 9 suka rage a gasar a nan gaba, kuma kullum kungiyar ta Leicester tana kara samun maki sannan sauran kungiyoyi masu harin matsayi na daya suna zubar da maki.

Abin tambaya dai a nan shi ne shin ko Leicester za ta iya daukar wannan kofi?