Chelsea: Likita ta kai kara kotu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Eva Carneiro da Jon Fearn a lokacin da suke duba Edwin Hazard a cikin fili.

Tsohuwar likitar kungiyar wasa ta Chelsea, Eva Carneiro ta bayyana a gaban kotu ta musamman kan korar ba-zata da Chelsea ta yi mata, abin da kira da cewa ya saba tsarin kwantaraginta da su.

Ana dai sauraron karar ne a kotun korafe-korafe ta musamman ta London South Employment Tribunal, a Croydon.

A watan Disamba ne dai Chelsea ta fara kare kanta daga zargin.

An kori Carneiro bayan da kociyan Chelsea, Jose Mourinho ya kalubalance ta tare da Jon Fearn saboda sun shiga fili domin duba lafiyar Eden Hazard

Hakan dai ya faru ne a lokacin wasan da suka tashi 2-2 da Swansea, a wasan farko na wannan kakar.