Samun jan kati laifina ne - Mata

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Juan Mata ya ce laifinsa ne da ya samu jan kati

Dan wasan tsakiya na Manchester United, Juan Mata ya dauki laifin samun jan katin da ya yi a wasan da West Brom ta ci su 1-0, ranar Asabar.

Shi dai Mata ya bar filin wasan ne bayan da ya samu yelon kati guda biyu a minti uku.

An fara ba wa Mata katin farko ne lokacin da ya nemi ya hana bugun tazara na gaggawa, a inda ya samu katin na biyu saboda keta da ya yi wa Darren Fletcher.

Mata ya ce " laifina ne saboda zan iya gujewa katinan."

Yanzu haka dai Juan Mata ba zai buga wasan dab-da-na-kusa-da-karshe da Man United za ta yi da West Ham ranar Lahadi ba.