Newcastle: Magoya baya sun rubuta wasika

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasikar dai ta fi mayar da hankali kan irin yadda kociyan Newcastle, Steve McClaren yake rike kulob din.

Magoya bayan kungiyar wasa ta Newcastle United sun rubutawa kulob din takardar koke dangane da kasancewarsa gab da ya bar gasar Premier.

takardar dai ta fi mayar da hankali wajen sukar kociyan kungiyar, Steve McClaren da 'yan wasansa.

Magoya bayan kulob din a cikin takardar sun ce "abin da magoya baya suke so shi ne samun 'yan wasa 11, wadanda suka san aikinsu a koyaushe."

A ranar Asabar ne dai Bournmouth ta ci Newcastle 3-1 a gida, al'amarin da ya mayar da kulob din na 19 a teburin gasar Premeir.

A ranar Litinin ne dai hukumar zartarwar kulob din suka zauna domin tattauna makomarsa da ta kociyan.