Newcastle: McClaren zai san makomarsa

Image caption McClaren dai yana fuskantar matsin lamba

Kociyan Newcastle, Steve McClaren zai san makomarsa nan da sa'o'i 48.

Shi dai McClaren yana fuskantar matsin lamba ne saboda kasancewar kungiyar ta 19 a teburin Premier.

Hakan na nufin kulob din yana fuskantar barazanar barin gasar karo na biyu, a tsawon shekara 7, bayan shan kaye sau 5 a wasanni 6 da suka hada da wanda suka tashi 3-1 da Bournmouth.

A ranar Litinin ne dai shugabannin hukumar gudanarwar kulob din suka zauna domin nemawa kulob din da kociyansa makoma.