Ramos ya goyi bayan Ronaldo

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ronaldo ne kashin bayan Real Madrid

Kyaftin din Real Madrid, Sergio Ramos ya bukaci magoya bayan Real Madrid da suka yi wa Cristiano Ronaldo ihu, su sake tunani.

Ronaldo ya zura kwallo daya sannan ya taimaka aka ci daya, a wasan da Real ta doke Roma da ci biyu da nema.

A cikin watan Fabarairu ne, alamu suka nuna cewa Ronaldo mai shekaru 31 na sukar abokan wasansa, amma daga bisani ya ce an yi wa kalamansa mummunar fahimta.

"Ina girmama magoya bayanmu, kuma ya kamata su ci gaba da nuna goyon bayansu ga 'yan wasa," in ji Ramos.

Ramos ya kara da cewa, bai fahimci abin da ya sa wasu magoya bayan Real ke sukar Ronaldo ba.