Emmanuel Eboue zai koma Sunderland

Image caption Kociyan Sunderland, Sam Allardyce

Kungiyar Sunderland ta rattaba hannu a kwantaragi na karamin zango da tsohon dan wasan baya na Arsenal, Emmanuel Aboue domin taka mata leda a karshen wannan kakar wasan.

Dan wasan dan kasar Ivory Coast wanda ba shi da kulob bayan da ya bar kungiyar wasa ta Galatasary da bazara, ya fara atasaye da Sunderland din a watan Fabrairu.

Eboue, mai shekara 32 wanda ya koma Arsenal daga Beveren a 2014, ya taka leda a Arsenal din har tsawon kakar wasanni 8.

A 2011 ne dai ya koma Galatasarey, a inda ya taimaka wa kulob din ya dauki kofin gasar Super League da kuma kofuna biyar na gasar cikin gida.