An sayar da Bolton Wanderers

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption kungiyar Bolton Wanderers a karawarsu da Liverpool

Rukunin Kamfanonin wasanni na Sports shield ya kammala sayen kulob din Bolton a kan Fam miliyan bakwai da rabi.

Tsohon dan wasan gaban kulob din Dean Holdsworth ne ke jagorantar rukunin, kuma zai kasance a hukumar gudanarwar kulob din, yayin da tsohon mai kulob din Eddie Davies, zai zama shugabansa na ban girma.

Ana bin kulob din Bolton bashin sama da fam miliyan 172, yayin da a watan Janairu wata Kotu ta ji cewa hukumar haraji ta Birtaniya na bin kulob din bashin sama da Fam miliyan 21.

Kulob din dai ya shiga halin matsin da ya sayar da filin horas da 'yan wasansa da kuma wurin ajiye motoci domin ya samu kudin shiga.