Tsohon dan Manchester zai koma gola

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tsohon golar Manchester zai yi wa tsohuwar kungiyarsa gola ne a wasan da za ta buga a ranar Asabar domin ya fitar ita kunya, bayan da golanta ya ji rauni.

Tsohon mai tsaror gida na Manchester United Edwin Van der Sar zai koma tsaron gida bayan ya yi ritaya.

Edwin dan shekaru 45 zai koma kame kwallo ne wa wata tsohuwar kungiyarsa bayan da mai mata tsaron raga ya samu rauni, shi kuma ya nuna aniyarsa ta taimakawa kungiyar da kuma fitar da ita kunya.

Tsohon mai tsaron gidan zai kama wa kungiyar tasa kwallo ne a karawar da za ta yi kulob din Jordan Boys a ranar Asabar.

Shekarar Van der Sar biyar a kungiyar VV Noordwijk ta kasar Holland kafinya ya koma Ajax yana dan shekara 20.

Kafin ya yi ritaya a shekara 2011 Edwin ya samu kyautukan yabo da yawa a gasar zakaru ta Netherlands da gasar Firimiya da kuma gasar zakarun Turai.