Mun shirya karawa da United — Klopp

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Klopp na tunanin za su girgiza United

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya ce wasansu na gasar Europa tsakaninsu da Manchester United "babban wasa ne na zakaru".

Manyan abokan hammayar a Ingila, za su fafata a karon farko a gasar Europa.

"Babban wasa ne, kuma watakila shi ne mafi girma a matsayi na na kocin Liverpool," in ji Klopp.

Manchester United ta lashe kofunan Turai sai uku a yayin da Liverpool ta lashe sau biyar.

Sauran wasannin:
  • Bor Dort vs Tottenham
  • Basel vs Sevilla
  • Fenerbahçe vs Sporting Braga
  • Shakt Donsk vs Anderlecht
  • Ath Bilbao vs Valencia
  • Sparta Prague vs Lazio
  • Villarreal vs Bayer Lev