Aguero zai bar Manchester City a 2019

Image caption Aguero na kewar Argentina

Dan kwallon Manchester City, Sergio Aguero ya ce zai bar kungiyar idan kwangilar shi ta kare a kungiyar.

Dan wasan na kasar Argentina, wanda ya kulla yarjejeniyar shekaru biyar a Etihad, kwangilarsa za ta kawo karshe ne a kakar wasan 2018 zuwa 2019.

Ya zura kwallaye 128 a City, tun lokacin da aka siyo shi daga Atletico Madrid a kan fan miliyan 38 a shekara ta 2011, sannan kuma ya lashe kofuna biyu tare da kungiyar.

Aguero mai shekaru 27, ya shaida wa gidan rediyon Argentina cewa "A nan City sun san abin da nake so, ina son in koma Argentina."