Scholes ya caccaki Manchester United

Scholes ya ce 'yan wasan United sun bada kunya

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Scholes ya ce 'yan wasan United sun bada kunya

Tsohon dan kwallon Manchester United, Paul Scholes ya bayyana kungiyar a matsayin "wacce ta shiga rudu" bayan da Liverpool ta doke su da ci biyu da nema a gasar Europa.

Scholes wanda ya buga wa United wasanni 718, ya ce "kwazon 'yan wasan ya ragu kamar ba su iya kwallo ba".

"Sun kashe fan miliyan 300 amma su ne na shida a kan tebur. An cire su a gasar zakarun Turai. Kamata ya yi su dinga goggaya da Barcelona, Real Madrid da kuma Bayern Munich.

Sakamakon wasu wasannin:

  • Bor Dortmd 3-0 Tottenham
  • Basel 0-0 Sevilla
  • Fenerbahçe 1-0 Sporting Braga
  • Shakt Donsk 3-1 Anderlecht
  • Ath Bilbao 1-0 Valencia
  • Liverpool 2-0 Man Utd
  • Sparta Prague 1-1 Lazio
  • Villarreal 2-0 Bayer Levkn