Odemwingie ya koma wasa Bristol City aro

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Peter Odemwingie tsohon dan wasan Super Eagles

Bristol City ta dauki Peter Odemwingie mai taka leda a Stoke City domin ya buga mata wasa aro zuwa karshen kakar bana.

Dan kwallon Super Eagles, ya kasa zura kwallo a raga a wasanni takwas da ya yi wa Stoke City.

Odemwingie ya koma Stoke City a Janairun 2014 inda aka yi musaya da Kenwyne Jones wanda ya koma Cardiff City da murza leda.

Kociyan Bristol Lee Johnson ya ce ya yi murna da Odemwingie zai buga musu wasanni, domin ya na da kwarewar da zai taimakawa kulob din.

Odemwingie wanda ya dade yana taka leda a Ingila, ya yi fice ne a West Brom inda ya ci kwallaye 31 a wasanni 90 da ya bugawa kungiyar.