Chelsea na bukatar sauye-sauye — Gullit

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea tana mataki na 10 a kan teburin gasar Premier

Ruud Gullit ya ce duk wanda aka bai wa aikin horar da Chelsea nan gaba yana da gagarumin aikin sauya yawancin 'yan wasan kungiyar.

Gullit ya ce idan ya kama John Terry da Eden Hazard da Diego Costa su bar kuniyar ko su ci gaba da zama, dole ne a sayo sabbin 'yan wasan da za su sauya salon wasannin da take yi.

Kociyan rikon kwaryar Chelsea, Guus Hiddink, wanda ya karbi aiki a wajen Jose Mourinho kafin kirsimeti, ya samu nasarori a wasannin da ya jagoranci kungiyar.

Sai dai kuma kociyan ya gamu da cikas inda aka cire ta daga gasar cin kofin zakarun Turai da kuma kofin Kalubale.

A ranar Asabar ne Everton ta ci Chelsea a 2-0 a gasar cin kofin kalubale da suka kara, kuma tsohon dan wasan Chelsea, Romelu Lukaku shi ne ya ci kwallayen.